Amurka da Burtaniya sun soki Shema

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Amurka da Burtaniya sun ce kalaman da Shema ya yi sun yi matukar muni.

Amurka da Burtaniya sun yi Allah wadai da gwamnan jihar Katsina ta Nigeria, Ibrahim Shema bisa kwatanta 'yan adawa da "kyankyasai", da cewa babu abun da ya cancanta da su illa kisa.

Sai dai gwamnan ya shaidawa BBC cewa ba haka yake nufi ba, ba a fahimci kalamansa ba ne.

A sanarwar da ofisoshin jakadancin Amurka da Burtaniya suka fitar sun ce kalaman sun yi matukar muni, kuma ba za a amince da su ba.

Sun yi kira ga 'yan Nigeria da su guji yin kalaman da za su yi sanadiyar tayar da hankali lokacin zabe da kuma bayansa.

A cewarsu, za su ci gaba da hada gwiwa da 'yan Nigeria wajen tabbatar da mulkin dimokaradiyya.

Sai dai a martanin da ya mayar, gwamna Shema ya ce bai ambaci sunan kowa ba a kwatancen da ya yi wa 'yan siyasa da kyankyasai, yana mai cewa 'yan adawa ne suka juya maganar domin bata masa suna.

Ya yi kira ga magoya bayansa da su guji tayar da hankula.

Karin bayani