'Abinda aka yi wa Tambuwal bai dace ba'

Image caption 'Yan majalisa na tsallaka hawa kofar shiga majalisar

Tsohon shugaban majalisar wakilan Nigeria, Alhaji Ghali Umar Na'abba ya bayyana yamutsin da aka samu a majalisar wakilan kasar a matsayin abinda bai dace ba.

A ranar Alhamis ne 'yan sanda suka harba wa 'yan majalisa barkonon tsohuwa ciki kuwa har da kakakin majalisar, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal.

Alhaji Ghali Na'abba ya ce irin wannan mataki, inda 'yan sanda suke cusgunawa jama'ar kasa ya na rage kimar Nigeria a idanun duniya, tare da shafar yakin da Nigeria ke yi da Boko Haram.

Tsohon kakakin ya ce kamata ya yi idan irin wannan abu ya taso a dunga taka-tsantsan, tare da sa kishin kasa a gaba.

A halin yanzu, 'yan majalisar wakilan Nigeria sun ce sun fara sanya hannu a kan wata takarda domin samun isasshen adadin wadanda za su amince a tsige shugaba Goodluck Jonathan.