Tambuwal ya karbi fom din takarar gwamnan Sokoto

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Tambuwal na son ya gaji Gwamna Wamako

Shugaban majalisar wakilai, Aminu Waziri Tambuwal ya karbi takardar neman izinin tsayawa takarar gwamnan jihar Sokoto a karkashin inuwar jam'iyyar APC.

Rahotanni sun ce shugaban majalisar ya bayyana cewar ya karbi fom din takarar ne sakamakon amsa kiraye-kirayen al'ummar jihar Sokoto.

A farkon wannan makon ne, Tambuwal ya yanke shawarar dakatar da aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin Nigeria a inuwar jam'iyyar APC domin, a cewarsa, a samu zaman lafiya da hadin kan jam'iyyar.

A karshen watan Oktoba ne Tambuwal ya sauya-sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC, abin da ya sa gwamnati ta janye masa jami'an tsaron da ke kare lafiyarsa.

A watan Fabarairun 2015 za a gudanar da zabuka a Nigeria.