Mayakan al-Shabab sun kashe mutane 28

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption A kwanan nan jami'an tsaro suka rika kai samame masallatai a Mombassa

Mayakan Islama na al-Shabab a Somalia sun ce sun kashe mutane 28 a wata motar safa a arewa maso gabashin Kenya.

An kwace motar safar wacce ke dauke da fasinjoji kimanin 60 a lokacin da take hanyarta zuwa babban birnin kasar Nairobi.

Wani fasinja ya fadawa BBC yadda aka ware 'yan Somalia da kuma wadanda ba 'yan Somalia ba, sannan aka harbi wadanda ba su iya karanta ayoyin kur'ani ba a kansu.

A wata sanarwa al-Shabab tace harin wani martani ne na kashe kashen musulmi da jami'an tsaron Kenya suka yi a garin Mombasa.