Google ya kaddamad da tallace-tallace kyauta

Kamfanin Google Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Kamfanin Google

Kamfanin Goolge ya kaddamad da wani shiri wanda ke tayin baiwa masu shiga internet zabin biyan kudi don shiga shafukka na tallace-tallace a maimakon ganin tallace-tallacen kawai.

Masu shiga internet din za su biya kudi kowanne wata tsakanin dala 1 zuwa 3 don shiga wadannan shafukka da ake tallace-tallace kyauta.

Lokacinda wadanda suka biya kudi don shiga irin wadannan shafukka kuma suka ziyarci shafukkan za su ga wasu alamomi na canjin tsarin shafukkan.

Kawo yanzu dai kamfanin na google ya cimma yarjejeniya da wasu shafukka da suka hada da ScienceDaily da Urban Dictionary domin gwada wannan tsari.

Wasu daga cikin shafukkan dake cikin wannan tsari sun hada da WikiHow da Imgur.

Damar shiga wannan tsari a yanzu sai dai shafin da aka gayyata kawai, duk wani shafi dake sha'awar shiga cikin shirin sai ya nemi a saka shi ciki, kuma sai ya jira a cikin layi.

Wani wanda ya bayar da gudumuwa ta bullo da wannan gwaji da za a yi, ya ce karin hanya ce ta samun kudin daukar shafin na internet.

Tallace-tallace ne a yau ke daukar nauyin Internet. To amma idan akwai wasu hanyoyi fana tallafa mutanen da suka kirkiro wadannan shafukka da ake shiga kodayaushe.

Kamfanin Google zai mori wani bangare na kudin, yayinda wani bangare zai je ga shafin na Internet da aka shiga ko aka kai ziyara.

Masu amfani da internet za su shiga ne ta shafin Google - daga nan shi kuma sai ya hada mutum da sauran shafukkan da yake bukatar shiga.

Karin bayani