An cafke masu kutse cikin kwamfutoci

Image caption Akwai 'yan Burtaniya 4 daga cikin wadanda aka cafke

An cafke wasu mutane 15, wadanda suka hada da 'yan kasar Burtaniya 4 bisa zargin yin kutse cikin kwamfutoci.

'Yan sanda suka ce mutanen suna amfani ne da wata manhaja da a ka tsara domin sarrafa kwamfutoci, wadda ta ke bada damar satar bayanai.

Sauran mutanen an cafke su ne a kasashen Estonia, da Faransa da Romania da Latvia da Italy da kuma Norway.

Sunan kusten "Ratting" wanda a wasu lokuta ya ke ba da damar satar bayanai daga na'urar daukan hoto da ke jikin kwamfutoci.

Wani shafin intanet da yake samun goyon bayan gwamnatin Burtaniya ya ce a na samun karuwar matsalar kutsawa na'urorin daukan hoto da ke jikin kwamfutoci inda a ke ganin mutane batare da saninsu ba.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Ana iya satar hoton mutane ta na'urar daukan hoto da ke jikin kwamfutocinsu batare da saninsu ba

Hukumar hukunta laifuffuka a Burtaniya ta ce ta cafke wasu maza biyu masu shekaru 33, da wata mata mai shekaru 30 a Leeds.

An kuna cafke wani matashi mai shekaru 20 a Chatham, sannan an gudanar da bincike a gidan wani mutun mai shekaru 19 a Liverpool saboda kutsen.

Mutane na fadawa tarkon masu kutsen ne a lokacin da a ke bukatarsu da su latsa wani wuri domin su kalli hoto ko bidiyo, inda wannan manhajar kutsen ke boye.

Za a iya kaucewa fadawa tarkon masu kutsen ne ta hanyar amfani da manhajoji masu kare kwamfutoci daga hadura.

Haka zalika, za a iya kauce musu idan mutane suka zamo masu taka tsantsan da mutane da suke fira da su a intanet.