WHO ta yi gargadin yaduwar Ebola a Mali

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Margaret Chan ta ce hukumar lafiya ta duniya ta na kara kaimi na dakile yaduwar cutar

Shugabar hukumar lafiya ta duniya, Margaret Chan ta yi gargadi a game da yaduwar cutar Ebola a kasar Mali.

Dr. Margaret Chan ta shaida wa wani taron 'yan jarida a Washington cewa a kwai bukatar a dakile yaduwar cutar kafin ta faskara.

Ta ce mutane dari biyar da suka yi mu'amala da wani Malamin addinin musulunci da ya kamu da rashin lafiya, ana sa musu ido.

Dr. Margaret Chan ta ce wasu mutane da suka fada hadarin kamuwa da cutar saboda haduwa da wata yarinya karama da take dauke cutar Ebola a kasar, sun haura kwanaki 21 da yakamata cutar ta nuna jikin su idan suna dauke da ita, ba tare da alamunta ba.