An kashe masu sana'ar kifi 50 a Doron Baga

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan kungiyar Boko Haram na cigaba da zafafa hare harensu

Kungiyar Boko Haram a Nigeria ta kai wani akan wani kauyen Masunta a garin Doron Baga dake Jihar Borno inda ta hallaka kusan mutane 50.

Wani dan kasuwa a yankin ya shaidawa BBC cewa maharan sun tsare hanyar da ke kaiwa kauyen ne inda suka hallaka wadanda ke kan zuwa sayen kifi.

Lamarin ya kawo jimmilar wadanda kungiyar ta kashe a kasar a 'yan kwankinnan zuwa kusan dari.

A ranar larabar da ta gabata, 'yan kungiyar sun kashe kusan mutane hamsin lokacinda ake cin kasuwa a wani kauye dake kusa da Maiduguri babban birnin Jihar ta Borno