Isra'ila zata koma kasar Yahudawa zalla

Hakkin mallakar hoto AFP

Majalisar Dokokin Israila ta amince da wani kuduri da zai maida kasar ta Yahudawa zalla.

Fryministan Kasar Binyamin Nathenyahu ya ce zai mikawa Majalisa Dokokin kasar wani tsari da zai taimaka mata a wajen aiwatar da wannan kuduri.

Fryministan ya kuma ce a karkashin sabon tsarin Yahudawa ne kawai keda 'yanci a kasar.

Masu adawa da wannan kuduri na ganin cewa idan har ya zama doka, to zai kaiga nuna bambanci ga labarawa 'yan kasar.

Kuma Antoni Janar na kasar ma ya ce yana ganin kudirin zai raunata tsarin domokradiyar a kasar.

Amma dai Fryminista Nathenyahu yace bai amince da wannan farbagar ba.