JNI ta caccaki gwamnati a kan tsaro

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kungiyar JNI ta ce wajibi ne gwamnatin tarayya ta kare rayuwar jama'a

A Najeriya, kungiyar Jama'atul Nasrul Islam ta kalubalanci gwamnatin tarayya a kan tabarbarewar tsaro a yankin arewa maso gabashin kasar.

Babban sakataren kungiyar, Sheikh Khalid Aliyu ya ce sun gaji da alkawuran da gwamnati ta ke dauka na magance matsalar amma batare da hakan ya yiwu ba.

Kungiyar ta bukaci gwamnatin kasar ta tashi tsaye wajen yaki da 'yan kungiyar Boko Haram masu tayar da kayar-baya, inda ta ce nauyin kare jama'ar Najeria yana wuyan gwamnati ne.

Kazalika, kungiyar ta Jama'atu ta yi Allah wadai da kashe-kashen jama'a da lalata dukiyoyi a arewa maso gabashin kasar.