Manhaja mai cutarwa a wayoyin Android

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Boyayyar manhajar NotCompatible ta na kara zama mai wuyar sha'ani

Dubban daruruwan wayoyin salula masu aiki da manhajar Android sun gamu da matsalar boyayyar manhaja mai cutarwa wadda take aikawa da sakonnin da ba a yi niyya ba da kuma sayen tikitin sha'ani a dunkule.

Kamfanin samar da tsaro a wayoyin salula, Lookout, ya ce boyayyar manhajar mai suna NotCompatible, itace mai cutarwa mahi wahalar sha'ani da kamfanin ya taba gani.

Masu sata a internet wadanda suka kirkiri manhajar, sun inganta ta kwanan nan ta yadda zata gagari mutane kauce mata.

Wani kamfanin samar da tsaro a wayoyin salula, Wandera ya ce boyayyun manhajoji masu cutarwa a wayoyin salula suna kara zama masu wuyar sha'ani.

Jeremy Linden, wani kwararre a fannin tsaron wayoyin salula ya ce wasu manhajojin masu cutar da wayoyin salula basa dadewa, amma masu amfani da NotCompatible sun haura shekaru biyu suna aiki da ita.

Ana yada boyayyar manhajar NotCompatible ne ta hanyar sakonnin da ba a yi niyyar aikasu ba, da kuma shafukan intanet wadanda a ke sauke abubuwa a kan wayoyi daga garesu.

Mr. Linden ya gargadi masu amfani da wayoyin Android da su yi hattara da duk wata manhaja da zata shafi tsarin tsaron wayoyi lokacin sauketa, kafin ta yi aiki.