An gano manhajar Regin mai cutarwa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Boyayyar manhajar Regin ta na satar bayanan sirri na bada damar shiga wasu shafukan mutane

Wani kanfani dake gaba-gaba a harkar tsaron kwamfuta ya ce ya gano wata boyayyar manhaja mai cutar wa a cikin kwamfutoci, wadda take daya daga cikin mafiya hadari da kamfanin ya taba gani.

Kamfanin Symantec ya ce manhajar mai suna Regin, mai yiwuwa gwamnati ce ta kirkire ta kuma anyi amfani da ita na tsawon shekaru shida a kan wasu da ake hako a duniya.

Da zarar aka dora manhajar Regin a kwamfuta, ta na iya daukar hoton shafukan da aka ziyarta, da kuma satar bayanan sirri na bada damar shiga wasu shafukan mutane.

Masana sun ce kwamfutoci a kasashen Rasha da Saudiyya da kuma Ireland ne suka fi fuskantar matsalar shigar manhajar ta Regin.

Masanan suka ce ana amfani da boyayyar manhajar ce wajen leken asirin hukumomin gwamnati da kasuwanci da kuma na wasu mutane.

Masu bincike sun ce kwarewar da aka yi amfani da ita wajen kirkirar manhajar ya nuna cewa gwamnatin wata kasa ce ta yi ta a zaman hanyar leken asiri.

Masu binciken suka ce aikin kirkiro manhajar ya dauki watanni biyu ko wasu shekaru ana yin sa, kuma wadanda suka kirkire ta sun yi nisa wajen hana mutane bin diddiginta.

Sian John, wani kwararre a kamfanin Symantec ya ce ''akwai alamu daga wata kasa ta yammacin duniya ne a ka kirkiri manhajar. Akwai kwarewa sosai a al'amarinta, da kuma tsawon lokacin da a ka ana aikin kirkirarta.

Kamfanin Symantec ya kimanta Regin da Stuxnet, wata boyayyar manhaja da ake tsammanin Amurka da Isra'ila suka kirkiro domin hakon shirin sarrafa nukiliyar kasar Iran.

An tsara manhajar Stuxnet ce ta lalata na'urori, yayin da aka tsara Regin domin ta saci bayanai.