Boko Haram: Mutane miliyan daya da rabi sun bar gidajensu

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dubban mata da kananan yara suna kwana a sansanonin 'yan gudun hijira

Majalisar Dinkin Duniya ta ce adadin mutanen da rikicin Boko Haram ya kora daga gidajensu sun kai a kalla mutane miliyan daya da rabi.

A cewar majalisar, adadin mutanen ya ninka har sau biyu cikin watanni shida da suka wuce.

Tun daga watan Yuli, kungiyar Boko Haram ta zafafa kaddamar da hare-hare, inda ta kwace garuruwa da dama a jihohin arewa maso gabashin kasar.

Ko a makon da ya gabata, Boko Haram ta kashe mutane kusan 100 a jihar Borno.

A nata bangaren, gwamnatin Nigeria ta ce tana iyaka kokarinta domin kawo karshen hare-haren da kungiyar Boko Haram ke kai wa a sassa daban-daban na kasar.

Ministan ayyuka na musamman Tanimu Turaki, ya ce ana cigaba da tuntubar wasu 'ya'yan kungiyar domin kulla yarjejeniyar tsagaita wuta.

A cikin watan da ya gabata, kungiyar ta Boko Haram ta musanta ikirarin da gwamnatin ta yi cewar sun kulla yarjejeniya.