Burtaniya na fuskantar barazanar ta'addanci

Theresa May Sakatariyar cikin gidan Burtaniya Hakkin mallakar hoto .
Image caption Theresa May Sakatariyar cikin gidan Burtaniya

Sakatariyar harkokin cikin gida ta Burtaniya Theresa May ta ce kasar ta fara fuskantar barazanar 'yan ta'adda tun harin da aka kai Amurka na 11 ga watan Satumba shekaru 13 da suka gabata.

Da take wani jawabi a London Mrs May ta bayyana sabbin matakan da za a dauka don magance matsalar ta'addanci a kasar.

Ta kuma ce a halin yanzu Burtaniya ta fara daukar matakai dan magance wannan matsala a fagage da dama;

Sakatariyar harkokin cikin gidan ta Burtaniya ta kuma zargi bullowar masu tada kayar baya da ke son kafa daular musulunci da karuwar ayyukan ta'addanci, wadanda suke daukar hankalin daruruwan musulmi 'yan Burtaniya.

Karin bayani