Chuck Hagel yayi murabus

Chuck Hagel Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Chuck Hagel

Sakataren harkokin tsaron Amurka Chuck Hagel ya bayyana aniyarsa ta yin murabus. Wani kakakin ma'aikatar harkokin tsaro ya ce Shugaba Obama ya amince da murabus din Mr Hagel.

An nada Chuck Hagel ne a shekara ta 2013 domin bullo da hanyoyin da za a rage kasafin kudi akan harkokin tsaro da kuma janye sojoji daga Afghanistan.

To amma wasu jerin rikice rikice a sassa daban daban na duniya da suka hada da rikicin Syria, da Cin zalin da Rasha ke nunawa a Ukraine da kuma barazanar da yan kungiyar ISIS ke yi na kafa kasar Musulunci, da alama sun yiwa gwamnatin Obama ba-zata.

Neman hanyar da ta fi dacewa wajen tunkarar wadannan matsaloli sun gwara kan wasu jami'ai ciki har da Mr Hagel da fadar White House.

Akan haka ne aka bada rahoton ya fara tattaunawa akan makomarsa a watan jiya. Mr Hagel, tsohon sojan da yayi yakin Vietnam ne, wanda kuma karfi kyautar yabon na ta Purple Heart, zai ci gaba da zama akan mukaminsa har sai an bayyana mutumin da zai gaje shi.

To amma a yanzu da majalisar dokoki ta ke hannun 'yan jam'iyyar Republican, mutumin da zai gaje shi na iya fuskantar babbar matsala gabanin a amince da shi.