An ba da tallafi ga asusun kula da yanayi

Alamar canjin yanayi Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Alamar canjin yanayi

Kasashe talatin dake yin taro a birnin Berlin sun yi alwashin bayar da tallafin kudi dala biliyan tara da miliyan dari 3 ga asusun kula da yanayi don taimakon kasashe masu tasowa rage hayaki mai haddasa dumamar yanayi da kuma shirya ma sauyin yanayi.

Kamata ya yi ace asusun kula da yanayin ya hada a kalla dala biliyan goma zuwa karshen shekara ta dubu biyu da goma sha-hudu, don haka alwashin nan kadan ya rage ya cimma wannan buri.

Asusun wanda hedikwatar sa ke Korea ta Kudu yana yunkurin taimaka ma kasashe ne su zuba jari a fannin samad da makamashi mai tsafta da kuma fasaha wadda ba ta cutar da yanayi.

Haka kuma an shirya zai taimaka ma su gina matarin ruwan teku da ambaliyar ruwan sama da kamfar ruwan.

Kasashe masu karfin tattalin arziki a can baya sun lashi takobin cewa zuwa shekara ta 2020 - kasashe masu tasowa za su samu dala biliyan dari daga wannan asusu ko wacce shekara.

Amurka ta rigaya ta yi alwashin bayar da dala biliyan 3, japan dala biliyan 1 da rabi Yayinda Jamus da Faransa sunka yi alwashin dala biliyan 1 kowaccensu, kasar Sweden za ta bayar da sama da dola miliyan dari biyar.

Akwai kasashe kamar Switzerland da Suth Korea da Netherlands da Denmark da Norway da Luxemburg da Jumhuriyar Czech da suka yi alwashin bayar da kudade kadan.

Bayan daukar nauyin taron na neman tallafi, Ministan Muhalli na kasar Jamus Gerd Mueller ya yaba da nasarar da aka samu, yana cewar lallai ne mutumtaka ta yaki sauyin yanayi yace, "bai kamata mutane su zamo kamar manyan kadangarun dinosaurs ba".

Daraktan asusun Hela Cheikhrouhou ya bayyana alwashin da aka yi na bayar da tallafin a matsayin wani sauyi na wasa, ya kuma ce za a kashe kudaden ne wajen magance abubuwan da sauyin yanayin yanayi ya haddasa musamman a kasashe masas sa karfi.

Wadannan dai sun hada da kasashe na kananan tsibirrai da kasashe matalauta na Afrika.

Karin bayani