Google ya warware rikicinsa da dan- kasuwa

Hakkin mallakar hoto PA

Wani dan kasuwar Burtaniya wanda ya kai kamfanin Google kara kotu game da wasu rubuce- rubucen batanci da akai akansa na batanci a shafin Google din, ya warware rikicin da kamfanin

Daniel Hegglin ya ce an yi kuskuren bayyana shi a matsayin mai kisa a shafin Google.

Lauyan Mr Hegglin ya fadawa Alkalin wata babbar kotu cewa Google ya yi yunkuri na cire cin mutuncin da akaiwa wanda yake karewa

Sai dai babu cikakken bayani game da yadda aka warware wannan rikici a ranar Lahadi

Mr Hegglin na son Google ya toshe wasu maganganu na batanci da aka rubuta akansa daga shafin kamfanin.

Warware wannan batu ya hada da wani yunkuri da Google ya yi na cire cin mutuncin daga shafukansa.

Mr Hegglin a yanzu zai maida hankali wajen neman hakkinsa a gun mutumin da ya rubuta kalaman batancin akansa

Wani jami'in kamfanin Google din ya ce kamfanin yana mu'amala da miliyoyin mutane, kuma ba zai iya daukar alhakin duba dukkanin irin abubuwan dake kunshe cikin shafukansa ba.

Mr Hegglin dai ya ce ya ji dadi sosai ganin cewar an warware rikicin