'Ba na kin jinin Musulmi' in ji Jonathan

Hakkin mallakar hoto Nigeria State House
Image caption Kungiyar MURIC na da ja a kan sabuwar takardar kudi ta naira 100

Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan ya ce ba ya amfani da ofishinsa wajen aiwatar da manufofin nuna kin jinin Musulmi kamar yadda wasu ke zarginsa da yin haka.

Kakakin Shugaban, Mr Reuben Abati ne ya bayyana hakan ga manema labarai a fadar shugaban kasar kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasar NAN, ya wallafa.

Fadar shugaban kasar na maida martani ne ga zargin da wata kungiyar musulmi mai suna, MURIC ta yi cewa Mr Jonathan na amfani da mukaminsa wajen yada akidum yahudawa.

Shugaban kungiyar MURIC, Farfesa Ishaq Akintola ya zargi gwamnati da saka wani tambari na alamar yahudawa a sabuwar takardar kudi na naira 100 da ya kaddamar.

A cewar fadar shugaban kasar zargin ba daidai bane, kuma tambarin da ake zargi ba na nuna akidar yahudanci bane.

Kakakin shugaban ya kuma jadadda cewar Mr Jonathan shugaba ne na kowa a kasar ba tare da bambamcin addinni ba.