Ana kone-kone a jihar Missouri ta Amurka

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu zanga-zanga sun lalata motocin 'yan sanda a St Louis

Ana zanga-zanga tare da kone-kone a yankin St Louis na gundumar Ferguson ta jihar Missouri a Amurka bayan da masu yanke hukunci suka ki tuhumar dan sandan nan farar fata da ya harbe wani matashi bakar fata har lahira.

Dan sandan mai suna Darren Wilson, ya harbe Michael Brown ne a yankin Saint Louis a watan Agustan da ya gabata, lamarin da haifar da mummunar zanga-zangar kwanaki da dama a yankin a jihar ta Missouri.

Babban mai shigar da kara a St. Loius ya ce, dama aikin masu yanke hukunci shi ne su bambamce karya da gaskiya.

Iyalan Michael sun nuna takaicinsu bisa wannan hukunci da aka bayar, amma sun yi kira ga mutane da su kai zuciya nesa.

A makon da ya gabata ne gwamnan jihar Missourin ya sanya dokar-ta-baci a jihar.

Yanzu haka an rufe makarantu da dama a yankin na St. Louis Talata domin gudun abin da ka-iya-biyo baya.