'Ba za a iya hana kashe Lee Rigby ba'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Adebolajo da Adebowale ne suka kashe Lee Rigby

Wani rahoto da majalisar dokokin Birtaniya ta fitar ya ce babu yadda za a iya hana kisan da aka yi wa wani sojan kasar, Lee Rigby a kusa da wani bariki da ke London.

An kashe Rigby ne a shekarar da ta wuce inda wasu musulmi biyu Michael Adebolajo da Michael Adebolawe suka kade shi da mota sannan suka kashe shi.

Mutanen biyu na cikin wadanda hukumomin tsaro irinsu MI5 da MI6 da kuma GCHQ ke bincike a kansu.

A yanzu haka an yanke wa mutanen biyu hukuncin daurin rai-darai a gidan yari.

Rahoton ya nuna cewa bai kamata a zargi jami'an tsaro da sakaci ba wajen kisan da aka yi wa Rigby.