Sirrin nasarar cinikin takalma a Ghana

Hakkin mallakar hoto Heel The World
Image caption Fred Deegba ya dauki ma'aikata 13 aiki a Ghana

Shirin African Dream wani tsari ne da ke duba nasarorin da wasu 'yan kasuwa daga nahiyar. Kowannensu zai bayyana irin kalubalen da ya fuskanta da kuma yadda kasuwancin ya habbaka.

Duk da cewar bai da ilimin yadda ake hada takalma, Fred Deegbe wanda tsohon ma'aikacin banki ne, ya lashi takobin zama babba mai kera takalma a duniya.

Tun bayan da ya hade da abokinsa suka kafa kamfani mai suna Heel The World (HTW) a shekara ta 2011 a Accra lekafa take ta ci gaba.

A yanzu kamfanin na da ma'aikata 13 domin kera takalma na sayarwa.

Ta yaya takalmanka ke goggaya da wadanda aka yi a China?

Hakkin mallakar hoto Heel The World
Image caption Daya daga cikin takalman da yake yi

Kayayyakin China ba abin damuwa ba ne gare ni. Saboda ina aiki ne da wasu tsare-tsare da ke taimakawa hajoji na:

  • Hamayya na da dadi amma akwai wuya. A don haka ina tabbatar da cewar ina kera takalma da babu wanda ke da irinsu a kasuwa.
  • Muna baiwa inganci fifiko ba farashi ba.
  • Ina maida hankali kan mutanen da ke son kayayyaki na musamman.
  • Ina tallata kayayyaki na a inda babu su.
  • Takalman da nake yi kirar hannu ne ba na inji ba.
  • Ina haba-haba da abokan hudda, saboda ta haka ne mutane ke sha'awar ci gaba da yi mani ciniki.
  • Daukar matasa masu kwazo aiki domin fito da samfuri iri daban-daban.
  • Jagorantar yekuwar kayayyakin da aka kera a Ghana saboda mutane su san mahimmancin kayan gida.
  • Hangen nesa. Ina yawaita tunanin yadda hajojina za su samu karbuwa tsakanin al'umma.