Majalisar dattawa ta yi watsi da dokar ta baci

Hakkin mallakar hoto davidmark facebook
Image caption Har yanzu a Nigeria ana cece kuce kan bukatar sake sanya dokar ta baci a jahohin arewa maso gabashin kasar.

A Nigeria, yau ne dai ake sa ran majalisar dattawan kasar za ta yi zama domin tattauna lamarin da ya kai ga 'yan sanda kai mamaye majalisar kasar, tare da harba hayaki mai sa hawaye a harabar majalisar.

A ranar Talata ne dai majalisar dattawan ta yi watsi da bukatar sabunta dokar- ta- baci da shugaban kasar ya gabatar mata, bayan wani zama na sirri da ta yi don jin ta bakin shugabannin hukumomin tsaro na kasar.

A yanzu dai 'yan majalisar dattawan sun ce batun sabunta dokar ta bacin babu shi, domin bisa tanadin kundin tsarin mulkin kasar dokar ta wuce, har sai in shugaban kasar ya sake aiko da wata bukatar ta sake kafa dokar.

Su ma 'yan majalisar wakilan kasar tuni sukai mahawara akan tsawaita wannan doka, kuma suka yi watsi da bukatar shugaban kasar.