Nigeria ta rage darajar naira

Hakkin mallakar hoto cbn facebook page
Image caption CBN ya ce baida zabin da ya wuce wannan

Babban bankin Nigeria-CBN ya rage darajar kudin kasar watau Naira sannan kuma ya kara kudin ruwa da mutane ke biya idan sun karbi bashin banki.

A yanzu bankin ya ce dalar Amurka daya zai yi daidai da naira 160-176 sabanin 150-160 da yake a baya.

Babban bankin ya ce rage darajar kudin kasar ya zama wajibi ne saboda faduwar farashin danyen mai a kasuwar duniya.

Tun a watan Nuwambar 2011 rabon da babban bankin ya rage darajar naira idan aka kwatanta da dalar Amurka.

Babban bankin kuma ya kara kudin ruwa daga kashi 12 cikin 100 zuwa kashi 13 cikin 100.

Gwamnan babban bankin kasar, Godwin Emefiele ya kare matakin a matsayin abin da ya fi dace wa a wannan yanayin da ake ciki.