Shari'ar amaryar da ta 'kashe' angonta a Kano

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Kakakin 'yan sandan Nigeria, Emmanuel Ojukwu

An ci gaba da sauraron shari'ar matashiyar nan mai shekaru 14 da ake zargi da kashe mijin ta, da kuma wasu mutanen uku ta hanyar zuba musu guba a abinci a jihar Kano.

Wannan ne dai karo na biyu da Wasila Tasi'u ke bayyana a gaban wata babbar kotun jihar Kano da ke zama a garin Gezawa.

Yarinyar dai wacce ake tuhuma da kisan kai na fuskantar hukuncin kisa, idan har kotun ta tabbatar da laifin da ake zargin ta da shi na kashe Umar Sani.

A zaman na ranar Talata, mai gabatar da kara, Lamido Abba Soron-Dinki ya gayyato wata yarinya Hamziyya wacce ta ce Wasila ta ba ta naira 80 domin siyo mata maganin bera.