An tashi baran-baran tsakanin Sufeton 'yan sanda da majalisa

Hakkin mallakar hoto Nigeria Police

An tashi baran-baran tsakanin 'yan kwamitin majalisar wakilan mai kula da harkokin 'yan sanda da kuma Babban Sufetan 'yan sanda, Sulaiman Abba,

Hakan ya faru ne a lokacin da Babban Sufetan 'yan sandan ya bayyana a gaban kwamitin a ranar Laraba.

'Yan majalisar sun zargi Sulaiman Abba da rashin girmama, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal a matsayin Kakakin majalisar a lokacin zaman.

Babban Sufetan dai ya bayyana a gaban kwamitin ne domin yi musu bayani kan baza 'yan sanda a majalisar tare da rufe wa kakakin majalisar da wasu 'yan majalisar kofa, sannan kuma suka harba musu hayaki mai sa hawaye.