"Ba mu yi nadamar fesa wa Tambuwal hayaki ba"

Hakkin mallakar hoto Nigeria Police
Image caption Suleiman Abba ya ce bai yarda cewa Tambuwal ne kakakin majalisar wakilai ba

Babban Sifeton 'yan sandan Nigeria, Suleiman Abba, ya ce bai yi nadama ba duk da barkonon tsohuwar da 'yan sandan kasar suka fesawa shugaban majalisar wakilan kasar, Aminu Waziri Tambuwal.

Ya bayyana haka ne lokacin da ya bayyana a gaban 'yan majalisar ranar Laraba a Abuja, yana mai cewa bai amince cewa Alhaji Aminu Tambuwal shi ne kakakin majalisar wakilan ba.

'Yan majalisar dai sun ce su ma ba su amince shi ne shugaban rundunar 'yan sandan kasar ba.

A makon jiya ne dai 'yan sandan suka fesawa 'yan majalisar barkonon tsohuwa -- cikinsu har da kakakin majalisar -- a yunkurin da suka yi na hana su shiga majalisar.

Karin bayani