An cire mataimakiyar shugaban Zimbabwe

Image caption Wasu masu goyon bayan Mujuru suma sun rasa mukaminsu a jam'iyyar

A kasar Zimbabwe, an cire ta mataimakiyar shugaban kasar, Joice Mujuru, daga cikin kwamitin zartarwa na jam'iyyar ZANU-PF mai mulkin kasar.

Hakan dai ya dakatar da burinta na siyasa a kasar ta Zimbabwe.

Ana dai zargin Mujuru da shirya makarkashiyar kashe shugaba Robert mugabe mai shekaru 90 a duniya.

Da ma dai akwai takun-saka tsakaninta da matar shugaba Mugabe, wadda ke neman ta gaji mijinta idan ya sauka daga shugabancin kasar.

Karin bayani