'Yan gudun hijirar Boko Haram sun yi zanga-zanga

Image caption Dubban mutane sun tsallake zuwa Kamaru

Daruruwan 'yan gudun hijira da suka tsere wa hare-haren kungiyar Boko Haram a yankin arewa maso gabashin Nigeria sun gudanar da zanga-zanga a gaban Majalisar dokokin kasar da ke Abuja.

'Yan gudun hijiran wadanda galibin su matasa ne, na kokawa da yadda mayakan kungiyar Boko Haram ke ci gaba da kwace wasu garuruwa tare da halaka jama'a.

Masu zanga-zangar sun shaidawa BBC cewar gwamnatin Nigeria ta yi juya musu baya ba ta taimakonsu.

Majalisar dinkin duniya ta ce kusan mutane miliyan daya da rabi ne suka rasa muhallansu sakamakon rikicin Boko Haram.

Dubban mutane kuma sun tsallaka zuwa makwabtan kasashe kamar Niger da Kamaru da kuma Chadi domin neman mafaka.