An hana jirgin Buhari sauka a Makurdi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Janar Buhari da matarsa a lokacin zaben 2011

An hana jirgin sama da ke dauke da tsohon shugaban Nigeria, Janar Muhammadu Buhari sauka a filin jiragen sama na Makurdi da ke jihar Benue.

Lamarin ya faru ne a ranar Laraba, lokacin da Janar Buhari ya baro birnin Fatakwal domin yada zango a Makurdi da zammar zawarcin 'ya'yan jam'iyyar APC su ba shi damar kasancewa dan takararsu a zaben shugaban kasa a 2015.

Wani na hannun damar Janar Buhari, watau Alhaji Faruk Adamu Aliyu ya tabbatar wa BBC afkuwar lamarin, inda ya ce jirgin saman na gabda sauka aka bayyana cewar an rufe filin jirgin saman Makurdi, a don haka jirgin saman bai da izinin sauka.

Hakan ya tilastawa Janar Buhari da wasu makarrabansa sauka a filin jirgin sama na Abuja.

Alhaji Faruk Adamu Aliyu ya ce lamarin ba zai sanyaya musu gwiwa ba, kuma suna shirin koma wa jihar Benue din domin zantawa da 'yan jam'iyyar APC a ranar Lahadi.

Janar Muhammadu Buhari na daga cikin mutane hudu da ke neman tikitin takarar shugabancin Nigeria a inuwar jam'iyyar APC.

Kawo yanzu hukumomin Nigeria ba su bayyana dalilan hana jirgin sauka a Markudi ba.