An samu rigakafin cutar Ebola a "matakin gwaji"

Hukumar da ke yaki da yaduwar cututtuka a Amurka ta yaba da samar da rigakafin cutar Ebola da aka yi a matakin gwaji, suna masu cewa ga dukkan alamu, allurar ba ta tattare da hadari.

Masanan sun ce mai yiwuwa maganin ya taimakawa garkuwar jikin dan adam wajen yaki da cutar ta Ebola.

Sai dai masu bincike sun ce sakamakon da aka samu ba cikakkiyar hujja ba ce na cewa maganin zai yi aiki, har sai gwaje- gwajen da za a yi a nan gaba sun nuna sakamako mai kyau.

Yanzu haka an yi ma wasu mutane 20 'yan kasar Amurka da suka mika kansu allurar riga kafin a hanzarin da ake yi na fara gwada tasirin allurar a jikin dan adam.