Bincike kan badakalar hodar Iblis a Ghana

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption A ranar 9 ga watan Nuwamba ne aka kama Nayele Ametefe a filin jiragen sama na Heathrow a London

'Yan adawa a kasar Ghana sun yi kira ga majalisar dokokin kasar da su yi bincike kan zargin kama wata mai safarar hodar Iblis da ta shiga masaukin shugaban kasa a babban filin jiragen sama na Ghana.

Wani dan Jam'iyyar NPP ya kai buhuhunan shinkafa uku masu nauyin 13kg majalisar, yana mai cewa ta yaya Nayele Ametefe za ta wuce da hodar iblis mai nauyin shinkafar zuwa cikin jirgi ba tare da an gani ba.

Shugaba John Mahama ya musanta hannun gwamnati a badakalar, kana ya ce matar ba ta da wani dangantaka da iyalinsa.

Ana tuhumar wasu jami'an Ghana uku da hannun wajen kyale matar ta yi amfani da masaukin shugaban kasar da ke filin jiragen sama na Kotoka da ke Accra.