Kungiyar IS ka iya sa wa mai ya yi tsada

Fadan da ake yi da kungiyar IS zai sa farashin mai ya tashi Hakkin mallakar hoto Getty

Hukumar makamashi ta duniya ta yi gargadi cewa rikicin da ake yi da kungiyar IS, mai ikirarin kafa daular musulinci zai iya sa wa farashin mai ya tashi a Iraqi.

Shugaban fannin tsimi na hukumar, Fatih Birol, ya shaidawa jaridar Financial Times, kungiyar tana hana kamfanonin mai su zuba jari a harkar hakar mai a kasar.

An sa ran cewa kasar ta Iraqi za ta samar da rabin ci gaban da ake samu a yankin, sai dai alkaluman baya bayan nan sun nuna cewa da wuya a samu hakan saboda rashin isassun kudi a wajen kasar.

Sai dai Mr Birol ya ce akasarin rijiyoyin hakar mai na kasar ba sa yankunan da ke hannun 'yan kungiyar ta IS.ISIS

Karin bayani