Kakakin majalisar dokokin Kebbi ya yi murabus

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Gwamnan Jahar Kebbi Sa'idu Dakingari

Kakakin majalisar dokokin jihar Kebbin Najeriya tare da mataimakinsa da kuma wasu manyan jami'an majalisar uku sun ba da sanarwar yin murabus daga kan mukamansu.

A ranar Alhamis ne Kakakin majalisar Hon. Aminu Musa Jega tare da wadannan jami'an suka sanar da ajiye mukamin nasu bisa abin da suka kira rashin adilci daga jam'iyyarsu ta PDP.

Sai dai jam'iyyar PDP a jahar ta musanta wannan zargi.

Tun a makon jiya ne dai ake danganta kakakin majalisar da mataimakin gwamnan jihar da shirin komawa jam'iyyar APC...

Amma daga bisani mataimakin gwamnan Alhaji Ibrahim Aliyu ya musanta hakan.