'Kalaman Obasanjo ba su yi mana dadi ba'

A Nigeria, wasu 'yan majalisar dokokin kasar sun maida martani kan zargin da tsohon shugaban kasar, Cif Olusegun Obasanjo ya yi musu na cin hanci.

Tsohon shugaban kasar ya ce cin hanci da rashawa sun dabaibaye bangaren zartarwa da majalisar dokokin kasar, abin da ya ke nuni karara da rashin sanin makamar jagorancin al'umma.

Sai dai wani dan majalisar Wakilai, Onarabul Ibrahim Bello Rigacikun, ya ce kalaman na Cif Obasanjo bai yi musu dadi ba.

'Idan da ya fadi haka, lokacin da ya samu dama ya yi mulkin kasar nan, mai yasa bai gyara ba' in ji Hon. Ibrahim Bello Rigachukun.

Wannan dai ba shi bane karo na farko ake zargin 'yan majalisar da cin hanci da rashawa.