'Yan bindiga sun kai hari a yankin Bani -Bangu na Nijar

Shugaba Mahamadou Issoufou na Nijar Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Mahamadou Issoufou na Nijar

A Jamhuriyar Nijar wani hari da wasu mutane da ba a san ko su wa ne ne ba dauke da makamai,suka kai,ya yi sanadiyar mutuwar mutane biyu dukansu farar hula.

Lamarin ya faru ne a Sabar-Bangu na yankin Banibangu da ke cikin jahar Tilabery mai iyaka da kasar Mali.

Maharan dai suna a kan babura ne lokacin da suka kai harin.

Wannan dai shi ne hari na uku da yan ta'adda ke kaiwa a yankin a cikin kasa da wata daya,inda jami'an tsaro da dama suka rasa rayukansu.

Wakilin yankin a majalisar dokokin kasar ta Nijar, Karimu Buraimah ya fada wa BBC cewar ya gaya wa gwamnati cewar akwai wasu dake shirin kai hari a yankin amma ba a dauki mataki ba.