Najeriya: An yi atisayen murkushe ayyukan ta'addanci

A Najeriya, an gudanar da wani atisayen gwaji game da yadda ake murkushe harin masu aikin ta'adanci a wuraren da ke samun cinkoson jama'a.

Jami'an tsaron daban daban da suka hada da sojoji da 'yan sanda har da na farin kaya da dai sauren su ne suka hallara a kasuwar Garki da ke birnin Abuja, inda aka gudanar da gwajin.

Wannan dai shi ne karo na farko da aka taba yin irin wannan gwajin kuma hukumomi sun ce za a ci gaba da yin irin shi a nan gaba a wasu bangarorin kasar.

Hakan kuma na faruwa ne yayin da Najeriyar ke fuskantar matsalar hare-hare da ke salwantar da rayukan mutane da dama.