Boko Haram:'Yan gudun hijira na tsallakawa Nijar

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan gudun hijirar Boko Haram

Hukumar 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce a kalla mutane hamsin ne aka kashe a arewacin Nigeria a cikin wannan makon a wani hari da 'yan kungiyar Boko Haram suka kai garin Damassak, da ke kan iyakar kasar da Nijar.

Hukumar ta ce kimanin mutane dubu uku ne a ka tilastawa tsarewa zuwa kasar ta Nijar.

Mutanen da suka yi gudun hijirar suka ce mayakan kungiyar ta Boko Haram sun harbi fararen hula, sannan kuma da yawa daga cikin wadanda ke gudun ceton rai sun mutu a cikin ruwa yayin da suke linkaya ketara wani rafi.

Hukumar 'yan gudun hijirar ta ce har yanzu, mata da yara kanana da kuma tsofaffi, suna jiran ceto a bakin rafin.

Wadanda suka samu tsira daga harin suka ce, an kai harin ne da nufin a hana maza matasa shiga kungiyoyin kare kansu, don yaki da kungiyar ta Boko Haram.