Kai Tsaye: Labarai kan harin da aka kai a Kano

Bayanai kai tsaye game da abinda ke faruwa sakamakon harin bam da aka kai a Kano

Latsa nan domin sabunta shafin.

5:00pm -- Bayanai sun ce bam din ya fashe ne gabanin a kai ga fara Sallah juma'a.

5:01pm -- Wani shaida ya ce ya girka gawawwaki kusan 200 a cikin asibiti a Kano.

5:06pm--- Hukumomi sun ce mutane kusan 64 sun mutu a yayinda fiye da 129 suka samu raunuka

Hakkin mallakar hoto Habibu Yahaya
Image caption Habibu Sani Yahaya ya aiko mana da hoton

5:10pm---- Habibu Sani Yahaya ya aiko mana da hoto

5:15pm---- Bayanai sun ce bayan tashin bam a Masallacin, sai wasu 'yan bindiga suka soma harin kan mai uwa dawabi.

5:17pm--- Babban masallacin dai shi ne inda mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na II ya ke Sallah inda a wani karonma shi ne ke yin limanci.

5:20pm--- Wasu majiyoyin sun ce Sarki Muhammadu Sanusi ya tafi Umrah a Saudiyya.

5:22pm---- Ana zargin 'yan Boko Haram da kai wannan harin a Masallacin Sarki.

5:30pm--- Wani shaida ya ce "Bayan an tada Sallah ana cikin ruku'u sai bam din ya fashe."

5:33pm---- A cewar ganau din "bama-bamai uku ne suka fashe a cikin Masallacin."

Ra'ayoyin Jama'a kan harin:

Image caption Dubban musulmi na Sallah a wannan Masallacin

Allah ya jikan wadanda suka mutu a harin bom da aka kai masallacin gidan sarki dake kano wadanda suka jikkata Allah ya basu lafiya.Daga Anas Saminu Ja'en Makera, Kano.

Nura Bello Darajakaset Gusau ko cewa ya yi "Al'ummar Kano muna jajanta muku dangane da fashewar bam a Masallacin Jumma'a da ke gidan sarki."

Image caption Wasu na ganin cewar an kai harin ne saboda Sarkin Kano

Adam A Adam Gashua cewa ya yi "Kaico Allah dai ya kawo mana karshen hare-hare da zubar da jinin al'umma a jihohinmu na arewacin Nigeria."

5:43pm--- Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya shawarci mutane su kare kansu daga hare-hare Boko Haram.

5:50pm--- Rikicin Boko Haram ra raba mutane kusan miliyan daya da rabi da muhallansu.

6:06pm--- 'Yan sanda a jihar Kano sun ce mutane 35 ne suka mutu sannan wasu da dama suka samu raunuka.