An kai harin bam a Masallacin Juma'a a Kano

Image caption Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu

Rahotanni daga jihar Kano a arewacin Nigeria na cewar wani abu da ake zargin bam ne ya fashe a kusa da babban Massallaci da ke gidan sarki a birnin Kanon.

Wadanda suka ganewa idanunsu abun da ya faru sun ce mutane da dama sun jikkata, inda suka ce ana wucewa da gawawwaki zuwa asibiti.

Bayanai sun ce bam din ya fashe ne gabanin a kai ga fara Sallah juma'a.

Babban masallacin dai shi ne inda mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na II ya ke Sallah inda a wani karonma shi ne ke yin limanci.

Rahotanni sun ce a yau dai Sarkin baya gari.

Harin na zuwa makonni bayan da Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya shawarci mutane su kare kansu daga hare-hare Boko Haram.