"Akwai dubban bayi a Birtaniya"

Theresa May, Sakatariyar cikin gida a Birtaniya Hakkin mallakar hoto .

Ma'akatar harkokin cikin gida a Birtaniya ta bada bayanan da a karon farko ke nuna yawan mutanen da ake rike dasu a yanayin bauta.

A bara an yi kiyasin cewa mutane dubu goma zuwa dubu goma sha ukku ne ke cikin bauta a kasar, amma yanzu ana ganin adadin ya ninka har so hudu.

Masu sukar lamirin gwamnati na zarginta da munafurci da kuma rashin maukafi, musanamna ma akan wadanda iyayen gidansu da suka yi dawainiyar kawo kasar ke bautar da su

Sakatariyar horkokin cikin gidan kasra ta ce lamarin mai tada hankali ne.

Yawancin wadanda ke bautar dai na aiki ne a gidajen mutane, ko gonaki, ko jiragen ruwa na musanta.

Wassunsu kuma suna karuwanci.

Ministar yaki da bautar zamani a kasar, Karen Bradley tace: Tace wannan mugun aikin, ana aikata shine a boye kuma dole ne a kawadda shi.

Yawancin wadanda ake bautarwan a cewar hukumomi, ana kawo su ne daga Najeriya, Vietnam da Romania.

Gwamnati ta ce zata tsaurara matakan sa ido akan iyakokin kasar domin hana shigowa da bayi.