Kotu ta wanke Hosni Mubarak daga zargi

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption An zargi Hosni Mubarak ne da kisan daruruwan masu zanga zanga

Wata Kotu a Masar ta wanke tsohon shugaban kasar, Hosni Mubarak bisa zargin kisan daruruwan masu zanga-zanga, a lokacin borenda da ya kifar da mulkin sa a shekarar 2011.

Kotun ta kuma kori shara'ar da a keyi wa wasu manyan jami'an gwamnatinsa.

A bara ne a ka yankewa tsohon shugaban kasar hukunci daurin rai-da-rai, amma sai ya daukaka kara.

Kotun ta kuma wanke 'ya'yansa da a ka tuhuma da cin hanci da rashawa.

Sai dai ana saran tsohon shugaban Masar din zai yi watanni a tsare saboda an same shi da laifin almundahana