'Fiye da mutane 100 ne aka kashe a Kano'

Hakkin mallakar hoto Babayo Tahir

Gwamnatin Jihar Kano a arewacin Najeriya ta ce akalla mutane 100 ne aka kashe a harin da aka kai a babban masallacin Juma'ar birnin.

An dai kai harin ne jiya a Kano lokacin da ake shirin fara sallar Juma'a a babban masallacin, wanda ke kusa da fadar sarkin Kano.

Sai dai wasu bayanai na nuna cewa daruruwan mutane ne suka mutu.

Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu, ya katse ziyarar da ya ke a Saudi Arabiya ya koma Kanon a ranar Asabar, inda ya jagoranci sallar magariba a masallacin.

Sarkin ya yi watsi da ikirarin cewa an kai harin ne saboda kiran da ya yi na cewa mutane su tashi su kare kansu daga hare-haren Boko Haram.

Ya kuma ce wadanda suka kai harin watakila sun kai wata biyu suna kitsa shi.

Shugaban Najeriyar, Goodluck Jonathan, ya sha alwashin gano wadanda suka kai harin.

A wata sanarwar da ya fitar, shugaban ya bayyana harin da cewa na rashin imani ne.

Karin bayani