Majalisar Nijar ta amince da kasafin kudi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban Mahamadou Issoufou na Nijar

Majalisar dokokin Nijar ta kammala zaman taron ta na watanni biyu da ya bai wa 'yan majalisar damar amincewa da kasafin kudi na 2015.

Majalisar ta amince da kasafin kudin na shekara mai zuwa wanda ya kunshi sama da biliyan dubu da 707 na cfa.

'Yan majalisar sun kuma yi na'am da wasu sabbin dokoki da suka hada da na bayar da takardar shedar zama dan kasa.

Haka kuma sun amince da dokar hana shigowa ko kasuwanci ko amfani da leda a kasar.

Majalisar dokokin ta yarda da wasu dokoki da suka bai wa gwamnati damar ciyo bashi daga waje.

Sannan ta amince da kara yawan 'yan majalisar dokokin Nijar din daga 113 zuwa 171 a zabe na gaba.

Sai dai kuma 'yan majalisar na adawa ba su halarci zaman ba saboda babban taron jam'iyyarsu.

Amma kuma Lamido Mummini Harouna na 'yan adawar ya soki majalisar game da kasafin kudin da cewa,kasafi ne na siyasa kawai.

Ya kuma zargi 'yan majalisar da cewa zama suke kamar na wasan kara.