Ebola ta kashe mutane 7000, inji WHO

Sabbin Al-kallumma daga Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, sun nuna cewa kusan mutane dubu bakwai ne Ebola ta hallaka, kuma yawancin su a yammacin Afrika suke.

Adadin yafi wanda hukumar ta ruwaito a makon jiya, inda ta ce kusan mutane dubu shidda ne suka mutu.

Cutar tafi hallaka mutane ne a kasar Laberia a cewar hukumar.

Ta kuma kara da cewa sama da mutane dubu 16 ne suka harbu da cutar kawo yanzu.

Cutar ta fi tsanani ne a kasashen yammacin Afrika da suka hada da Guinea, da Saliyo da kuma Laberiya.

Kasashe dadama na kai taimakon ma'aikata da kayan aiki zuwa kasashen da fama da cutar.