Ana cafke masu zambar sayen tikitin jirgi

Jirgin sama Hakkin mallakar hoto ATI
Image caption Jirgin sama

Ana kai samame filayen jiragen sama don cafke masu sayen tikitin hawa jiragen sama ta hanyar zamba.

Masu satar bayanan katin banki na mutane ta internet suna sayen tikitin jirgi sune aka dumfafa a samame da dama da aka kai filayen jiragen sama.

'Yan sanda ne na kungiyar Tarayyar Turai suka shirya samamen a filayen jiragen sama inda suke cafke mutanen dake kokarin sayen tikiti da bayanai na katunan mutane da suka sata ta internet.

A jimlace, an cafke mutane 118 wadanda aka cafke a filayen jiragen sama 80 a kasashe 45 a lokacin samamen.

Rundunar 'yan sandan ta Tarayyar Turai ta ce, Kamfanonin jiragen sama suna hasarar sama da dola billiyan 1 ko wace shekara ta hanyar sayar da tikiti da bayanai na boge na katin banki.

A cikin wata sanarwa, Meta Backman ta kungiyar kare zambatar kamfanonin jiragen ama ta ce, a kulli yaumin, kamfanonin na jiragen sama suna yaki ne da mazambata sayen tikitin da bayanai na katunan mutane da suka sata.

Tace, "wani abu ne da ya fito karara cewar kamfanonin jiragen saman suna yaki ne da wata kungiya mai karfi ta masu satar bayanan katunan banki na mutane."

Rundunar 'yan sandan ta Turai tace, wannan samame shine farkon matakin da aka dauka wanda aka yi ma lakani da "daukar matakai na yaki da mazambata a filayen jiragen sama na duniya".

Wannan matakin ne zai hada jami'an 'yan sanda da ma'aikatan jiragen sama da kamfanoni masu bayar da katunan banki a shire-shiren samamen da za a rinka kai ma irin wadannan mutane.

Gama kai tsakanin wadannan hukumomi ne zai taimaka wajen gane lokacin da aka sayi tikiti da katunan banki na wasu da aka sata a samamen da aka kai na kwanaki biyu. Daga nan ne 'yan sanda za su yi awon-gaba da mutumin da ya sayi tikitin ta hanyar zamba.

Cibiyoyin bayar da umurni da aka kakkafa a Hague da Singapore da Bagota sun taimaka wajen binciken tikitin da aka saya ta hanyar zamba da takardun tafiya na boge da kuma gane wurinda mutanen da aka kame suka fito.

Wasu daga cikin mutanen da aka cafke 'yan sanda ma sun rigaya sun san su, an kuma rigaya an cafke su kafin su kai ga sayen tikitin.

Karin bayani