Birtaniya: Bankin Barclays zai kawo sauyi

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Bankin ya ce wannan tsari shi ne na farko a harkar banki a Birtaniya

Bankin Barclays na Birtaniya zai fara bai wa masu mu'amulla da shi damar magana da ma'aikatansa kai tsaye ta bidiyo.

Tsarin na nufin mai mu'amulla ko ajiya a bankin zai iya yin magana kai tsaye da ma'aikaci a kowana lokaci.

Mai ajiyar zai iya magana da ma'aikacin bankin ta wayarsa ta salula ko kwamfutar hannu da sauransu.

Wani babban jami'in bankin Steven Cooper, ya ce, tsarin wani gagarumin ci gaba ne da sauyi a harkar banki a Birtaniya.

Jami'in ya ce, tsarin na nufin masu ajiya za su yi mu'amulla da bankuna yadda suke so ba yadda bankunan suka ga dama ba.

Hakkin mallakar hoto 1

Za a fara aiwatar da tsarin ga masu harka da bankin akan harkar gidaje da kasuwanci da kuma sauran fannin dukiya daga farkon 2015.

Daga nan ne kuma za a fadada shi ga dukkanin masu mu'amulla da bankin.

Mr Cooper ya ce, wannan tsari zai bai wa masu mu'amulla da bankin damar magana keke-da-keke ta bidiyo da ma'aikacin bankin.

Abin da ba a ko da yaushe mai ajiya ko mu'amulla ke samun damar tattauna da jami'in banki ba.