An fasa gidan yari a Ado Ekiti

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Gidan yarin Koton Karfe da aka fasa a watan Nuwamba

'Yan bindiga sun fasa babban gidan yari na jihar Ekiti a kudancin Nigeria, lamarin da ya yi sanadiyyar tserewar wasu fursunoni.

An kai hari a gidan yarin wanda ke Ado Ekiti babban birnin jihar ne a cikin daren ranar Lahadi.

Rundunar 'yan sandan jihar Ekiti ta tabbatar da aukuwar lamarin, amma kakakinta Victor Olu ya ce tuni aka damke wasu daga cikin fursunonin da suka tsere.

Kawo yanzu babu tabbas a kan wadanda suka kaddamar da harin.

A cikin watan Nuwamba ma an kai hari a wani gidan yari da ke Koton Karfe a jihar Kogi inda fursunoni fiye da 50 suka tsere.