Gwamnati ta ce ba hannunta a Boko Haram

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mataimakin shugaban Najeriya, Namadi Sambo ya ce, su 'yan arewa ba za su bari a ci zarafin yankin ba

Gwamnatin Nigeria ta musanta zargin da wasu ke yi cewa tana da hannu a hare haren da mayakan kungiyar Boko Haram ke yi a arewacin kasar.

Mataimakin shugaban kasar Arc. Namadi Sambo wanda ya futo daga yankin arewacin ya ce babu yadda 'yan yankin da ke cikin gwamnati musamman a fannin tsaro za su bari a yi wani abu da zai cuci al'ummarsu.

Namadi Sambo dai na magana ne a lokacin da ya jagoranci tawagar gwamnatin kasar a ziyarar ta'aziyya da jaje da suka kai Kano, sakamakon hare haren da aka kai ranar Juma'ar da ta gabata.

A nasa bangaren, sarkin Kano Alhaji Muhammad Sanusi na biyu ya yi kira ga gwamnatin kasar da a gano masu hannu a hare haren ta hukunta su.