Ana taro kan sauyin yanayi a Peru

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Sauyin yanayi ya kasance babbar barazana ga duniya

Wakilai daga kasashe sama da 100 sun fara taro kan yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya game da sauyin yanayi a yau Litinin a Lima, babban birnin Peru.

Makasudin taron shi ne cimma yarjejeniya domin rage yawan iskar gas mai dumama yanayi.

Masu sharhi kan sauyin yanayi sun ce akwai alamun cimma yarjejeniya, bayan Amurka da China sun amince cewa za su rage yawan tiririn da ke dimama yanayi a farkon wannan watan.

Ita ma kungiyar kasashen Turai ta sanya shekara ta 2030 domin ganin an rage yawan fitar da iskar gas din.

Sai dai kuma mahalarta taron za su fuskanci matsala wajen fitar da daftarin da za a yi amfani da shi a taron da za a yi a Paris a shekara 2015, lokacin da za a cimma matsaya domin rage fitar da iskar gas mai sauya yanayi.

Za a kwashe kimanin mako biyu ana wannan taro.