Boko Haram: Ƙura ta lafa a Damaturu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Gwamnati ta ce an kori 'yan ta'adda daga cikin birnin

Kura ta dan lafa a Damaturu babban birnin jihar Yobe bayan da aka wayi gari da jin karar harbe-harben bindiga da fashewar wasu abubuwa.

Lamarin ya jefe mutane cikin zullumi a yayinda dakarun kasar na sama da na kasa suka kare birnin daga munanan hare-haren na 'yan Boko Haram.

Kakakin gwamnan jihar Yobe, Abdullahi Bego ya shaidawa BBC cewa "Jami'an tsaro sun taka rawar gani inda suka fatattaki 'yan ta'adda."

Bego ya kara da cewa "Abubuwa sun lafa a gari kuma jiragen sama kusan hudu na ta shawagi tare da luguden-wuta."

'Yan Boko Haram da ake zargi da kaddamar da wannan harin, sun kona wani barikin 'yan sanda a Damaturu.

Babu cikakkun bayanai kan adadin wadanda suka mutu sakamakon harin.

Kungiyar Boko Haram ce keda iko da garuruwa da dama a jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa.